Za a iya samun bayanan magun guna a wannan shafin, domin kare kanmu daga cuttutukan da suka shafi rayuwarmu tayau da kullum.
Tuesday, May 21, 2019
ALAMAN CIWON SIGA
LAFIYA UWAR JIKI: Alamomi 13 na ciwon siga (Diabetes)
'''''''''''''''''''-----------------''''''''''''''''''''
Lafiya uwar jiki kamar yanda masu iya magana ke cewa, wannan zamani da muka tsinci kammu a ciki inda jama'a basu cika damuwa da ababen da suke ci ba, musamman kayan qwalam da maqulashe, hakan ta kai ga jama'a na kamuwa da cutuka daban daban.
Daya daga cikin cutukan shine CUTAR SIGA (Diabetes), wanda ke nufin cewa halin da sigar dake jikin mutum tayi yawa fiye da adadin da jiki ke buqata.
Ana iya gane hakan ne idan an lura da:
* Yawan jin qishirwa
* Yawan bushewar fata da qaiqayi
* Yawan bushewar baki
* Yawan futa fitsari da daddare
* Yawan kasala
* Yawan jin yunwa matsananciya
* Gani dishi-dishi
* Qiba
* Lalacewar ciki
* Rashin samun nutsuwa
* Ciwo ga jijiyoyi
* Dadewa ciwo ko rauni bai warke ba.
Yana da kyau idan mutum yaga mafiyawancin wadannan alamomi to ya qauracewa cin nau'o'in abinci kamar haka:
* Masara
* Farar shinkafa
* Burodi
* Dankali
* E.t.c
sai dai yana da kyau ya dinga cin nau'o'in abinci kamar haka:
* Alkama
* Tumatir
* Ayaba
* Naman Tala-talo
* Kashu
* Abarba
* Wake
* Karas
* Lemu
* etc.
Amma fa babbar shawara itace a garzaya assibiti domin ganin likita.
Malaria
Maccen sauro kadai Allah ya nufa data yada wannan ciwo na malaria, Allah ya halacci macen sauro da wasu ababen al'ajabi
1, Allah ya halacci macen sauro da idanu fiye da dari 100,
2, Allah ya halacci macen sauro da wani sanadarin kashe zafi wato anesthesia, duk lokacin da Maccen sauro zata ciji Dan adam saita zuba wannan acid din sannan ta ciza koda mutum zaikai bugu har ta tashi, baxakaji zafin cizon ba sai ta tashi a jikin ka
3, mancen sauro Allah yayi ta da wani sifirin wanda komi kaurin fata saita huda ta lokacin da take so.
Mu Kare kanmu daga kamuwa da zazzabin cizon sauro ta hanyar anfani da gidan sauro mai dauke magani damu da iyalan mu gaba daya.
Mu zama masu rufe toilets da daddare.
Mu kasance muna rufe Kayan ajiyar ruwa da rijiyoyinmu.
Mu kasance muna nome ciyawa a gidajen mu, Sanna mu fidda magudanun ruwa.
Mu kaucewa yin shuka a gidajen kwana da kuma Gyara kwata kwata a gidajen mu.
Allah ya Kare mu daga zazzabin malaria.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment