Monday, May 20, 2019

FA'IDOJIN NONON RAKUMI

FA'IDOJIN NONO RAKUMI.
Assalamu Alaykum ya nyan uwana musulmai ga kadan daga cikin fa'idojin Nonon Rukumi daga bakin sheikh Hassan Ackadi, Malami kuma Likita (Doctor) a bangaren Likitanci Na addinin musulunci Wanda yake da zama Garin Tawa dake cikin kasar Niger. Allah ya saka masa da Alkairi. Ameen.
GABATARWA:
Alhamdulillah yau kuma zamuyi bayani akan fa'idojin Nonon rakumi, Wanda yake dauke da fa'idojin masu dunbum yawa, kuma da sinadarai, vitamin masu yawa da sauran abubuwan da suke taimakawa jikin Dan Adam. Wanda Manzon Allah da kansa ya bada umurnin anfani da wannan Nono mai Albarka. Allah yasa sanya Albarka a cikin wannan littafi Wanda shine littafin na shida a jerin littatafai mu daga wannan cibiya mai Albarka.
FA'IDOJIN NONON RUKUMI:
1. Yana kiyaye lafiyan jikin Dan Adam baki daya.
2. Yana kubutar da jiki daga cholesterol.
3. Yana magance bacteria masu cutarwa.
4. Yana kula da na'ura mai kula da ruwan jiki.
5. Yana magance rashin lafiya na tumbi.
6. Yana magance kumburi.
7. Yana magance rashin lafiya na Colon.
8. Yana magance matsalan hanta.
9. Yana magance rashin lafiya na shawara.
10. Yana magance ciki in yana kwasan ruwa.
11. Yana magance tarin Tb (tuberculosis).
12. Yana magance matsalan saifa.
13. Yana magance matsalan rashin jini.
14. Yana magance matsalan Yawan jiki.
15. Yana da fa'idojin masu yawa ga mata masu ciki.
16. Yana karfafa kashin dan Adam.
17. Yana magance matsalan gyembo da kurarraji da duk wani matsalan fata.
18. Yana karfafa gashin dan Adam.
19. Yana magance da kare mutum Daga cancer(Daji).
20. Yana karfafa hakora.
21. Yana magance rashin lafiya na dasoshi.
22. Yana daidaitar da diabetes a jikin Dan Adam.
23. Yana magance matsalan zuciya.
24. Yana magance matsalan hawan jini.
25. Yana karfafa na'ura mai kula da gabobi.
26. Yana magance shawara.
27. Yana magance matsalan nunfashi.
28. Yana magance matsalan basur.
29. Yana kula da na'ura mai kula da ruwan jikin dan Adam.
30. Yana magance matsalan raunin mazakuta.
31. Yana magance rashin haihuwa.
FITSARIN RAKUMI:
32. Fitsarin rukuma yana magance kumburin hanta.
33. Yana magance matsalan fata.
34. Ya magance matsalan gyembo da kuraje.
35. Yana magance karkaryewan gashi idan anasha.
36. Yana magance rashin lafiya na tumbi (ulcer) da hakora.
37. Anfison anasha Nonon ko fitsari da safe kafin karyawa ko shiga bacci amma zaka iya sha Koda yaushe.
38. Ga Wanda basu da lafiya anfiso susha kafin fitowan rana da kuma bayan faduwanta.
39. Ina diban karamin Kofi da ake shan Sha'i Wanda bai wuce cokali uku ba.
40. Yana magance cututtuka viruses.
41. Yana kare garkuwan jikin Dan Adam.
42. Yana magance ciki in yana kwasan ruwa.
43. Yana magance ciwon kirji.
44. Yana magance rashin lafiya na tsufa.
45. Yana karfafa kashin dan Adam.
46. Yana magance sanko idan anasha ana kuma shafawa.
47. Yana karfafa hakora.
48. Yana kula da lafiyan hanta da saifa.
49. Yana magance dunkulewan jini.
50. Magance matsalan nunfashi.
HANYOYIN DA AKE MAGANCE MATSALOLIN LAFIYA:
MAGANCE MATSALAN IDAN KANA FITSARI KANA JIN ZAFI DA ALAMOMIN DAZA KANAJI:
1. Jin zafi a karkashin maranka.
2. Jin zafi yayin fitsari.
3. Ko kayi fitsari zakana Ji kamar akoi saura.
4. Yawan jin zungure zungure a hanyan fitsari.
5. Baiyana jini a cikin fitsari da ruwa lokacin da kake fitsari.
6. Zakana Yawan yin fitsari da dare, haka da rana ma.
7. Zakana jin wani wari ya fitowa daga Fitsarin.
8. Yana sanya Yawan zafin jikin mutum ya hauhawa.
9. Yana sanya mutum rufewan zuciya. Dajin Amai.
10. Yawan jin mafitsara tana cike Koda kayi fitsari.
ABUBUWAN DA SUKE SANYA WANNAN MATSALAN:
1. Kwayoyin bacteria da suke shiga hanyoyin fitsari ko jini.
2. Jinkirta yin fitsari Koda kana jinsa.
3. Banke bahaya kafin fitsari.
4. Karuwan nishadin bacteria ta mafitsara.
5. Komawa fitsari zuwa iretur. Misali kana ciki fitsari ka yanke ya koma.
6. Mata masu ciki.
7. Shigowan tsakuwa mafitsara.
8. Bacteria idan suka shiga hanyoyin kodan dan Adam.
9. Rashin lafiya na ciwon sugar ( diabetes) da sauran su.
HANYOYIN RIGAKAFI DA MAGANIN MATSALAN:
1. Ka yawanta shan abubuwan sha da Yawan shan ruwa.
2. Ka nisanci kamuwa da kumburi.
3. Kana zuwa fitsari kafin kwanciya bacci.
4. Kana shan ruwa kafin jima'i in ka gama kaje kayi fitsari.
5. Ka nisanci sabulan da turawa suke bugawa don yin wanka ta Al'airanka.
6. Kana yin fitsari kusa da kusa.
7. Ka nisanci duk abunda aka hada kamar su kafe da sauran su.
MAGANI:
1. Kana Yawan shan juice na tuth.
2. Ana kula da tsafta na jiki.
3. Anasha ruwa Kofi guda da cokali guda na khal tuffa.
4. Ana shan tafasasshen ruwan bagdunus asa Zuma asha da yawa.
5. Ana anfani da habbatus sauda.
6. Ana shan tafasasshen ruwan Bazurul kitan Kofi uku a rana.
7. Arr Arr asamu mansa ana digawa a cikin babban cokali na sugar Sai aci safe da yamma.
8. Ana dafa furawula anasha safe da yamma har Sai an samu lafiya.
9. Ana dafa Sha'ir a ruwa anasha Kofi daya sau uku a rana.
10. Ana dafa citta asha Kofi guda da safe guda da yamma anasa Zuma a ciki.
11. Asamu habbatus sauda Rabin Kofi, Zuma Kofi guda da Tafarnuwa guda uku da aka daddaketa a gauraya su. Sai a raba gida uku asha safe, rana da maraice.
12. Asamu iccen Hindiba'a a dafa anasha kamar Sha'i ko anasawa a cikin kayan yamutse ana ci. Wannan sune hanyoyin da ake bi don magance matsalan mafitsara.
KAMMALAWA:
Alhamdulillah anan muka kawo karshen wannan littafi mai suna fa'idojin Nonon rakumi da kuma matsalan mafitsara kuma shine littafin mu na shida muna fatan Allah yasa ya anfani Al umman musulmi a duk inda suke a fadin duniya ameen.
DON NEMAN KARIN BAYANI:
Ga masu Neman Karin bayani zaku iya tuntuban shehin Malami akan wadannan layuka kamar haka:
96679943, 90306526, 94857939. Amma wadanda suke wajen kasar Niger zasuyi anfani da daya daga cikin codes din nan +227, 009227 or 00227. Kuma zaku iya Neman wa'azuzzukan Malam akan YouTube idan kuka rubuta "MALAM HASSANE ACKADI" a search box. Za'a hadaku da jerin karatuttukan sa. Ga kuma link dinsa na zuwa kan karatuttukan sa:
WALLFAWA,
Dan uwanku a musulunci kuma daya daga cikin almajiran Malam Hassan Ackadi wato:
MOHAMMED ABUBAKAR MUBI.

No comments:

Post a Comment