Za a iya samun bayanan magun guna a wannan shafin, domin kare kanmu daga cuttutukan da suka shafi rayuwarmu tayau da kullum.
Saturday, May 18, 2019
AMFANIN BAURE
MAGUNGU NAN DA BAURE YAKEYI.
Daga Ahmad Rabiu Saraki
Ana sarrafa baure ta hanyoyi daban daban don gabatar da biyan bukata ga kadan daga ciki
(1)Basur Wanda bayajin magani asamo "ya"yan baure da man zaitun a hadashi da leman tsami sai a sanya su acikin Abu mai kyau ajika abarshi ya kwana da safe sai atace ashanye duka.
(2)Ciwon koda asamu baure ajikashi da ruwa kofi 3 ashanye a yini daya.
(3)Ciwon jijiya da basur mai tsiro a hada ganyen baure da nonon baure akwaba adinga shafawa agun ayini daya.
(4)Yawan Rama ba tare da wani daliliba-arika zuba garin baure a kunu anasha
(5)Karye war gashi-a kwaba garin ganyan baure da man shanu ana shafawa akai
(6)Ciwon farfadiya asamu kisdul Hindi da dakakken yayan baure ahada da Zuma ana sha kullum sau daya arana
(7)Domin samun lafiyar ciki-da yayan baure anayin shayin sa anasha har tsawon kwana 4 ko kuma arika sha duk lokacin cin abinci.
(8)Ciwon dan karkare-a samu ganyen baure da garin yayan da garin ruman a kwaba anasha fawa a yatsun adaure yatsan insha Allah zaiyi ruwa yafashe da wuri ya warke.
(9)Tautau ko kazuwa-a samo nonon baure a hada da toka ana shafawa safe da yamma insha Allah za adace.
Domin Karin bayani sai ku tuntubemo a number waya kamar haka.08160799455.Naku malam Ahmad
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment