Monday, May 20, 2019

ALAMOMIN SHIGAR CIKI

ALAMOMIN SHIGAR CIKI
:::::: :::::
wadanne alamu mace za ta gani idan tana dauke da sabon ciki ta yadda za ta gane tun kafin taje asibiti.
Ba kowace mace ce ta kwana da sanin cewa babban abin dake kawo 6atan wata shine samun juna biyu ba. Bayan juna biyu kuma cutukan shigar kwayoyin cuta mahaifa sune kan gaba wajen kawo batan wata, ko rikicewar lissafin wata (haila).
Sauran sun hada da shayarwa, yawan damuwa ko ciwon damuwa, da rashin zama wuri daya ko rashin samun hutu, kamar masu wasanni masu tsanani, wasu lokuta ma har da shan wasu magunguna barkatai walau na asibiti ko na gida.
TOH WADANNE ALAMU MACE ZATAJI TA TABBATAR CIKI NE?
GASU A ZAYYANE:- A watannin farko mace za ta yi 6atan wata, bayan yan satuttuka, sai ta fara samun tashin zuciya da sassafe har da amai a wasu lokuta, ko da ma ba a ci komai ba. Sauran alamun sun hada da saurin gajiya, idan an yi wani dan aiki ko jin jiri, idan an zo mikewa.
To a wannan lokaci ne ake so a je a yi gwajin juna biyu a tabbatar ta hanyar auna fitsari, a yi hoton ciki, idan ma cikin ne a tabbatar a mahaifa yake ba a waje ba.
A watannin da ciki ya fara tsufa kuma, kamar ya kai wata uku, akan ga alamu kamar haka: Girman ciki, yawan jin fitsari ko zaryar yin fitsari, saboda abin da ke ciki ya fara danne marar fitsari. A wasu akan samu ciwon baya, da ciwon kirji wato zafin kahon zuci ko kwarnafi saboda ‘acid’ din ciki na tasowa a kirji.
Sai kuma a fara samun duhun fuska da fitowar zane a fatar ciki, da budewar hanci a wasu da kuma nauyi ko ciwon mama. Ba dole ba ne kowace mace ta samu dukkan wadannan alamu, amma kusan rabin mata suna samun a kalla rabin wadannan alamun.
Ibrahim Y. Yusuf

No comments:

Post a Comment