Monday, May 20, 2019

AMFANIN WAYAN NAN ABU BUWAN

AMFANIN IDON ZAKARA DA IDON SHANU DA WUYAN DAMO DA NONON KURCIYA DA DAI SAURANSU.
Sunayen wasu tsirrai da Hausa da kuma amfaninsu ga lafiyar al'uma.
Daga cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, masu yin Ruq'yah da harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700, 08134434846.
1) Idon Zakara:- Yana maganin typhoid, maganin zazza6i, yana kara jini, yana rage radadin ciwo sannan yana da kyau wajen abinda ya shafi kwanciyar aure, ga mata.
2) Nonon Kurciya:- Yana maganin gudawa, cututtukan da ake dauka yayin saduwa, ciwon kansa, dafin kunama, da maganin namijin dare ga mata.
3) Tubanin Dawaki:- Yana maganin zazza6in Maleria, gudawa, cututtukan kwakwalwa, ciwon ido, ciwon kunne, da saran maciji.
4) Qaimin Qadangare:- Yana magance cututtukan fata, maganin gudawa, ciwon hakori na yara, ciwon koda kuma yana maganin matsalolin Aljanu.
5) Zaqi-banza mai qaya:- Yana magance cututtukan maqogwaro, maganin tari, ciwukan kansa, cututtukan fata, qunar wuta, maganin zazza6i da kuma matsalolin numfashi.
6) Kashin Yawo:- Yana maganin gudawa, saukake fitowar hakori na yara, ciwon ciki, ciwukan fata da kuma zazza6i.
7) Takalmin Binta:- Yana maganin ciwon nono.
8) Kargon Allah:- Matsalolin ciki, ciwukan zuwan jinin al'ada, ciwon qoda da kansa da kuma maganin gudawa.
9) Rai-rai / Rai-dore:- Yana maganin Typhoid, Maleria, matsalolin mara, hawan jini, tsakuwar ciki da kuma cutar basir.
10) Wuyan Damo:- Yana maganin ciwon mara, matsalolin zuwan jinin al'ada da kuma maganin tari.
11) Ka-fi-Mallam:- Maganin matsalolin ciki.
12) Nonon Kura:- Maganin saran Maciji.
13) Fidda Sartse:- Yana maganin ciwon kafa, ciwon kai da kuma cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa.
14) Kurar Shanu:- Tana maganin ciwon Kansa da matsalolin fata.
15) Bi-ni da zugu:- Maganin yoyon fitsari, cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa, ciwukan yayin zuwan al'ada, da kuma cutar typhoid.
16) Mikiya:- Tana magance ciwon hauka, maganin gudawa, matsalolin fata, zazza6i, ciwon kai da kuma sanyin jiki.
17- Ka fi Amarya Qamshi:- Yana kashe dafi, yana maganin ciwon hauka da zazza6in Maleria, tana maganin matsalolin Aljanu.
18- Zabuwa:- Maganin ciwon ciki, qonewar fata, ciwukan fata, warkar da ciwo cikin sauri, tana kuma maganin ciwukan ido dana kunne.
19) Abin kan iyaka:- Yana kara jini, rage matsalar hawan jini, da kuma maganin cizon maciji.
20) Fasa Kumburi na mace:- Yana maganin zubar jini, ciwon mara, gudawa, cutar cancer, cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa da kuma cutar asthma.
21) Fasa kumburin namiji:- Yana magance matsalolin ciki, tari, asthma, yana tsaftace jini, yana maganin ciwon qirji da basir.
22) Kai dubu:- Yana maganin cutar Hauka (mental illness).
23) Farin Ruwa:- Yana maganin cutukan sikila da Maleria.
24) Qaiqayi koma kan masheqiya:- Yana maganin cizon maciji, maganin gudawa, kuma yana maganin Aljanu da sihiri.
25) Kuru-kuru:- Yana maganin ciwon koda da matsalolin ciki kuma yana rage radadin ciwo.
26) Goga masu:- Yana kara jini, yana maganin asthma, cututtukan fata, basir, cututtukan da ake iya dauka yayin saduwa, ciwon koda, sikila, tsattsagewar qafa da matsalolin ciki.
27) Wuta-wuta:- Tana kashe kwayoyin cuta, tana maganin sikila, tana rage radadin ciwo sannan tana maganin ciwon suga.
28) Taba-taba:- Tana maganin ciwon hauka.
29) Idon Shanu / Gautan kura:- Yana maganin ciwon Hauka.
Qarin bayani.
Dukkan wadannan tsirrai ne da ake iya samunsu a kasar Hausa, musamman Arewacin Nigeria, don haka ko ina za ka iya samunsu, wajen masu magungunan gargajiya.
Wadannan tsirrai mun fadi amfaninsu ne amma in kana bukatar kasan yadda ake sarrafa su, ka iya tuntu6ar lambobin wayar da aka bayar a qasa ko kuma duk wanda ka samu maganin a hannunsa.
Binciken amfanin wadannan tsirrai, mun yi shi ne akan tsarin *Binciken maganin gargajiya ta hanyar zamani*, don haka fa'idodi ne da aka tabbatar da su ta hanyar binciken likitanci na zamani.
Ba daidai bane wani ya cire mana lambobin wayarmu ya saka tasa ko sunan cibiyarsa. Don haka akula da masu satar fasaha suna tallan magani alhali ba su san maganin ba.
Allah Ya sa mu dace Amiyn.

No comments:

Post a Comment