Sunday, May 19, 2019

MATAKAN KARIYA DAGA CIYON HANTA

MATAKAN KARIYA DAGA KAMUWA DA CUTAR HANTA (HEPATITIS) Yadda kamuwa da cutar hanta ta zama ruwan dare sakamakon rashin daukar wasu matakai, jama'a ku karanta wannan jawabin sannan ku sanar da iyalai da 'yan uwa da masoyanku, sannan ayi sharing duk inda ya dace Ina ma ace mutane zasuyi hakuri su daina amfani da cokali, kofi, lemun kwalba, pure water, kai duk inda dai yawun bakinka zai hadu da na wani ina ma ace jama'a sun dauki matakin kiyayewa daga yau?! Musamman a wajen mai shayi, idan mutum daya mai cutar hanta (hepatitis) yasha shayi ya gama, zakuga nan take mai shayin zai saka kofin a cikin ruwa ya girgije sannan yayi amfani da kofin ya zuba wa wani, to ya zuba kwayoyin cutar hanta a cikin ruwan da ya girgije kofin wancan mai dauke da cutar hanta, kuma duk kofin da za'a 'kara wankewa da wannan ruwan za a iya daukar wannan cuta ta hepatitis Cutar hanta gata nan tayi yawa a asibiti, ana ta mutuwa kuma mutane basu san ta inda suke samunta ba, haka mai sayar da abinci a restaurant ko hotel, haka mai dafa indomi, haka kofi na shan ruwa na kowa da kowa da akan ajiye a wajen aiki ko masallatai na kasuwa, duk wani abun amfani wanda zaisa yawun bakin mutum zai hadu da na wani wallahi a kiyaye mu'amala dasu jama'a Akwai sauran guraren kamuwa da cutar hanta kamar yin jima'i da wanda yake dauke da cutar, sannan sumba (kiss) da saka tufafin da mai dauke da cutar ya saka kuma gumin jikinsa ya taba tufafin, a kiyaye jama'a! Kuma dayawan mutane suna da cutar hanta amma basu san suna da ita ba, kuma basu san cewa suna yada ta a cikin al'umma ba, cutar hanta ba a saurin gane wanda yake dauke da ita a ido, sai idan tayi nisa sosai a jikin mutum musamman wanda baya zuwa gwaji asibiti Yana da kyau duk bayan watanni 7 mutum ya dinga zuwa asibiti ana masa gwajin cutar hanta, ana iya maganin cutar hanta da zaran an ganota idan batayi tsanani ta kai wani mataki ba, don haka zuwa gwaji a asibiti yana da matukar muhimmanci DON HAKA JAMA'A AYI HATTARA A KIYAYE (HEPATITIS) CUTA CE MAI SAURIN KISA Kar a manta ayi sharing don sauran jama'a su amfana Allah Ka karemu daga kamuwa da cututtuka masu saurin kisa Amin.

No comments:

Post a Comment