Friday, May 24, 2019

MAGANIN SHAKUWA

INA MASU FAMA DA SHAKUWA? TO GA HANYAR DA ZA'A BI DON MAGANCE TA CIKIN SAUKI
*********************************************
Shakuwa itace shakewar makogoro(makoshi) kokuma mutum ya ji kamar wani abu ya toshe masa makoshi, sai yayi wata kara mai kama da gyatsa don ya samu sa'ida.
Ba koda yaushe akan yi shakuwa ba sai dai wasu mutanen takan zame musu cuta, sai suyi tayinta koda yaushe.
YANDA ZA'AHADA MAGANIN:-
Asamu goruba akona ta har kwanlon dake ciki sai adaka atankade.
YANDA ZA'AYI AMFANI DA MAGANIN:-
Arika zuba coka daya acikin kunu asha sau biyu arana zuwa mako guda.
KARIN BAYANI:-
Wannan maganin yana magance asima, amma masu fama da asima zasu zuba cokali daya na maganin acikin shayi, su sha sau biyu arana zuwa kwana 14.

No comments:

Post a Comment