Tuesday, May 21, 2019

CUTAR INNA

MAGANIN CUTAR IN-INA: Itadai in-ina cutace wacce take hana mutum furta wasu lafuzza ayayin da yake magana, Ko kuma ta haifarwa mutum da jinkiri wajan furta wasu lafuzza, Akwai wanda saboda tsananin in-ina harsai ya zubda hawaye kafin ya iya furta magana ko lafazi. IN-INA TA KASU KASHI BIYU. 1- akwai wacce ake haihuwar mutum da ita (wato wacce mutum ya gada kenan). 2- akwai wacce mutum yake kamuwa da ita rana tsaka tun yana karami ko kuma bayan girman sa. NAU'IN IN-INAR DA AKE WARKEWA: In-inar data samu mutum rana tsaka tun kuruciya ko kuma bayan girman mutum itace muke magana akanta. MAGANINTA. Kasamo Zuma mai kyau ingantacciya, Yar gida ba yar waje ba, sai ka samo gishiri. Ka cakuda zumar da gishirin ta inda dandanon gishirin zai bayanna acikin zumar, amma ba mai kama baki ba. YADDA ZA'A SHA. Za'a sha sau Biyu a rana, kafin karin kumallo da kuma lokacin kwanciya bacci da daddare. NB. Ba lokaci guda ake warkewa ba a'a, sai anjure amfani da maganin ahankali waraka zata zo, Inshaa Allah. Kuma wannan maganin mutane dayawa sun gwada kuma sun dace. Allah yasa adace Amin. Don Allah inka karanta kayi sharing don wasu suma su amfana, kaima kasamu Ladan.

No comments:

Post a Comment